Addini

Ramadaniyyat 1443 [2] : Masu Tauye Mudu [2] – Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo

Ci gaba a kan fashin baqi game da ayoyin farko na Suratul Mudaffifina:

*Ba Su Kadai Ne ba:

9. Waɗannan ayoyi, duk da cewa, suna yin magana ne a kan tauye mudu ko sikeli, to amma ba iya kan wadannan ma’aunan maganar ta tsaya ba. Dukkan wani tauye hakki, kowane iri ne, ya shiga ƙarƙashin wannan ayar; ko da kuwa ba ta hanyar awo da sikeli ko mudu ba.

*Sauran ‘Yan Kasuwa Da Masu Sana’ar Hannu:

10. Duk wasu ‘yan kasuwa da masu sana’ar hannu za su iya shiga karkashin wannan ayar, kamar masu sayar da yadi ko kuma masu sana’ar ayyukan hannu; kamar magina ko makera, ko kanikawa, ko masu aikin wutar lantarki ko hada famfo, da sauran ayyukan hannu. Idan aka ba dayansu aiki amma sai ya cuci wanda ya ba shi aikin, watau ya ƙi inganta aikinsa yadda ya dace, ko wasu abubuwa da ya kamata ya siyo masu inganci, sai ya siyo marasa inganci, ko ya karɓi kuɗin kayayyaki masu kyau sai ya siyo marasa kyau, amma kuma ya karvi lissafinsa shi cif-cif, to wannan babu shakka ya shiga cikin wannan aya, azaba mai tsanani tana jiransa.

A Zamantakewa Aure:

12.Hakanan a zamantakewa ta miji da mata. A ce miji kullum yana son matarsa ta ba shi haƙƙoƙinsa cikakku, amma shi ta bangarensa yana tauye mata nata haƙƙoƙin, ta wajen ci ko sha ko sutura, to wannan shi ma ya shiga cikin ƙarƙashin wannan ayar.

13. Ita ma matar da take neman haƙƙinta a wajen mijinta, amma ba ta kiyaye haƙƙoƙin shi mijin nata, ta fuskar yi masa biyayya da kyautata masa tarbiyyar ‘ya’ya da dauke masa dawainiyar aikace-aikacen cikin gida, to ita ma tana cikin wannan aya.

*Tsakanin Uba Da ‘Ya’yansa:

14. Hakanan uba da ‘ya’yansa, yayin da uba zai riƙa neman haƙƙinsa a wajen ‘ya’yansa, amma ya shi kuma ya ƙi kula da su wajen ba su kyakkyawar tarbiyayya, amma kuma yana so su yi masa biyayya, to babu shakka shi ma ya shiga cikin wannan aya.

15. Su ma ‘ya’ya masu naman haƙƙinsu a wajen iyayensu, amma su kuma ba sa bayar da haƙƙin iyayensu a kansu, to duka za su shiga cikin wannan ayar.

Tsakanin Shugabanni Da Talakawansu:

16. Hakanan shugabanni da talakawansu, yayin da talaka zai rika neman shugaba ya ba shi haƙƙinsa, amma shi kuma ta ɓangaransa ba ya ba wa shugaba nasa haƙƙin, watau ya ki yi masa biyayya, ya ki sa shi a cikin kyakkyawar addu’a, ya ki yi masa nasiha inda ya kamata ya yi masa nasiha ta hanyar da ta kamata, amma kuma kullum maganarsa daya ita ce kakkokinsa da suke kan shugaba, ba ya maganar haƙƙin shugaba a kansa. To ba shakka wannan ma ya shiga karkashin wannan ayar.

17. Hakanan shugaban da kullum yake tunanin haƙƙoƙinsa a kan talakawansa, watau yana son su bi umarnin da dokokinsa, su ba shi girmansa, amma kuma shi ya yi biris da nasu hakkokin dake kansa, ba ma ya son maganar sam-sam, to duk waɗannan suna shiga ƙarƙashin wannan ayar, watau suna neman haƙƙinsu cikakke amma sun yi watsi da wanda yake a kansu.

18. Saboda haka zaman lafiyar ɗan’adam shi ne ya kula da haƙƙin mutane. Ana ma son shi ya zamanto mai haƙura da nasa haƙƙin, watau idan ya ba wa mutane hakkokinsu, shi sun hana masa nasa to, ya yi hakuri ya nema a gurin Allah (S.W.T). Domin bawa ya je ga Allah yana bin wasu bashin hakkokinsa, ya fi masa alheri a kan ya je masa da hakkokin wasu a kansa. Annabi (S.A.W) ya yi nasiha ga talakawa waɗanda Allah ya jarrabe su da azzaluman shugabanni masu cutar da su da cewa:
“Ku ba su haƙƙoƙinsu dake kanku, ku kuma ku nemi Allah ya ba ku naku haƙƙin” [Duba, Sahihul Bukhari#3603 da #7052 da Muslim#1843].

19. Watau ku ba su haƙƙoƙinsu na saurare da yi musu ɗa’a, da girmamawa, ku kuma Allah (S.W.T) zai karɓo muku haqqoqinku a wurinsu.

20. Amma idan ya kasance shugabanni sun hana talakawa haƙƙokinsu, suma talakawa sun hana shugabannin haƙƙoƙinsu, da sunan cewa ramawa suke yi, to dukkansu sun zama ɗaya a wurin Allah (S.W.T).
To lalle wannan aya gargaɗi ne da ya shafi kowa da kowa.
Allah ya sa mu dace.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button