Addini

Ramadaniyyat: 1443 [15]Sai An Sha Wuya Akan Sha Daɗi (2) – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo.

1. A labarin da Khaɗibul Baghdadi ya bayar na Al-Imam Ibrahim bn Ishaƙ Al-Harbi (285H) ya ruwaito mana shi yana cewa: “Duk masu hankalin cikin kowace al’umma sun yarda da cewa, duk wanda bai tafi tare da ƙaddararsa ba, to ba zai ji daɗin rayuwarsa ba. Nakan kasance da rigata mafi tsafta, amma kwarjallena kuma yakan zamo mafi dattin kwarjalle. Ban taɓa ji a raina cewa za su daidaita ba samsam. ƙafar takalmina guda a tsinke take, guda kuma mai lafiya. Amma kuma da su, a sanye a ƙafuna, nake kewaya garin Bagadaza kakaf, ban taɓa tunanin zan gyara su wata rana ba. Ban taɓa koka wa mahaifiyata cewa ina zazzaɓi ba, hakanan ban taɓa faɗa wa ‘yar’uwata ko matata ko ‘ya’yana mata irin haka ba. Namiji shi ne mai barin damuwarsa a ransa, ba ya yarda ya jefa iyalansa cikin damuwa. Ina fama da ciwon tsagin kai na tsawon shekara arba’in da biyar amma ba wanda na taɓa faɗa wa. Shekara goma ina gani ne da ido ɗaya, amma ba wanda ya sani. Yanzu shekara talatin da biyar ke nan abincina gurasa ce guda biyu, idan mahaifiyata ko ‘yar’uwata ta kawo min in ci, idan kuwa ba su kawo ba, sai in kwana da yunwa da ƙishirwa…”. [Duba, Al-Khaɗib, Tarikhu Baghdad, juzu’i na 6, shafi na 522 (Basshar)].

2. Babu shakka wannan yana nuna mana yadda wasu kaɗan daga cikin mazan jiya, sukan nuna halin ko-inho da wahalhalun da suke fama da su, domin cimma wani babban burinsu a rayuwa.

3. Wannan labarin na Ibrahim Al-Harbi, shi ne Ibn Taimiyya ya taƙaita mana a cikin wasu taƙaitattun kalmomi, inda yake cewa, “Ibrahim Al-Harbi yana cewa, ‘masu hankalin cikin kowace al’umma sun haɗu a kan cewa, ba a cimma samun ni’ima ta hanyar ni’ima’. [Ibn Taimiyya, ƙa’idatun Fil Mahabba, – Majmur Rasa’il, juzu’i 2, shafi na, 393].

4. Sau tari duk wani jin daɗin duniya ba ya samuwa sai an sha wuya, kamar yadda Shaikhul Islam Ibn Taimmiya ya bayyana. [Duba, Majmu’ul Fatawa, juzu’i na 20, shafi na 146].

5. Kuma babban abin da zai ƙara wa mutum ƙaimi da ƙarfin gwiwa da jure wa duk wata wahala, shi ne ya riƙa tuna irin daɗin da zai biyo baya bayan wahalarsa ta ƙare. Masana suna cewa, ‘Gwargadon wahalarka gwargwadon cika burinka’.

Za mu ci gaba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button