Addini

Ramadaniyyat: 1443 [14]Sai An Sha Wuya Akan Sha Daɗi (1) – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Advertisment

1. Manyan buruka da suka danganci rayuwar ɗan’adam ta fannin ilimi da shugabanci da kasuwanci da tarbiyyar al’umma da kawo gyara; duk waɗannan buruka ba za su samu ba sai bayan an sha wuya an kuma jigata matuƙa.

Ramadaniyyat: 1443 [14]Sai An Sha Wuya Akan Sha Daɗi (1) - Dr Muhammad Sani Umar R/lemo
Ramadaniyyat: 1443 [14]Sai An Sha Wuya Akan Sha Daɗi (1) – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo
2. Idan ka ga wani malami yana ruwan ayoyi da hadisi, yana kutsawa cikin mas’alolin ilimi yana bayin su abin sha’awa, to kada ka taɓa tsammanin cewa, cikin sauƙi da hutu da jin daɗi ya cimma wannan matsayi.

3. Hakanan idan ka ga attajiri ya yi suna a fagen kasuwanci, ya shahara wajen yawan dukiya da kadarori, to kada ka taɓa tsammani cewa, shi a da mutum ne da ya saba wa idanunsa barci a duk sanda yake so, ko wanda ya gina rayuwarsa a kan zaman kashe wando da hutu.

4. Imamu Muslim, babban malami ne masanin ilimin hadisan Manzon Allah (SAW). Ya rubata shahararren littafinsa wanda aka fi sani da suna: Sahihu Muslim. Tsarinsa a wannan littafin shi ne, amboton hadisan Annabi (SAW) zalla. Ba ya kawo maganganun sahabbai balle na tabi’ai a cikinsa.

Advertisment

5. Bayan ya gama rubuta hadisin Abdullahi ɗan Amru game da tantance lokutan salla. Ya tattara hanyoyinsa da mabanbanta lafuzansa, sai kawai a ka ga ya ruwaito maganar wani tabi’i mai suna Yahya bn Abi Kasir yana cewa, “Ba a iya samun ilimi da hutun gangar jiki”.

6. Wannan abu da Imamu Muslim ya yi a nan ya ɗaure wa masana kai, domin sun kasa gane alaƙa tsakanin hadisan da ya kawo a wannan babin da maganar wannan tabi’i. To amma Shehun Malami Alƙali Iyad ya ruwaito sirrin cusa maganar wannan tabi’i a daidai wannan wuri daga wani malaminsa, inda ya bayyana masa manufar Imamu Muslim a wannan wuri da cewa, watau shi kansa Imamu Muslim ya yi sha’awa da mamakin abin da ya rubuta a wannan mahalli, sai ya ƙara fahimtar irin gwargwadon wahalar da ya sha wajen tattaro waɗannan bayanai. Don haka ne ya kawo maganar Yahya bn Abi Kasir, domin ya nuna wa mai karatu cewa, babu mai kai wa ga irin wannan ilimi sai ya sha wuya.

7. Duk wata kamala a rayuwar ɗan’adam, ba za ta samu ba sai bayan an sha wuya. Kamar yadda Ibnul ƙayyim yake cewa: “Dukkan wata kamala ba ta samuwa sai an sha wani kaso na wuya. Ba kuma za a iya ƙetarawa zuwa gare ta ba sai ta kan kadarkon wahala”. [Duba, Ibnul Kayyim, Miftahu Daris Sa’adah, juzu’i na 2, shafi na 895].

Za mu ci gaba insah Allah….

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button