Addini

Ramadaniyyat: 1443 [13]Tausaya wa Halittun Allah – Dr Muhammad Sani Umar R/leno

1. An karvo daga Abdullahi ɗan Amru (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Masu tausayi, (Allah) Mai Rahma zai tausaya musu, ku tausaya wa waɗanda suke bayan ƙasa, sai wanda yake sama (Allah) ya tausaya muku”.
[Abu Dawud #4941 da Trimizi #1924, da Ahmad #6494].

2. A wannan hadisi Annabi (SAW) ya yi kira da a tausaya wa duk wata halitta da Allah ya yi, mutane ne ko dabbobi. Don haka ka zamanto mai tausaya wa kanka, mai tausaya wa wasu. Kada ka zama ɗan tsako samu ka ƙi dangi.

3 Ka ji tausayin ƙarami da babba. Ka tausaya wa jahili da iliminka. Ka tausaya wa talaka da dukiyarka. Ka tausaya mai sabo da wa’azinka. Ka tausaya wa komai har dabbobi.

4. Duk wanda tausayinsa ga halittun Allah ya yawaita, to zai dace da tausayin Mahaliccinsa. Allah zai shigar da shi gidan karamci da ɗaukaka, sannan ya tsare shi daga azabar ƙabari, ya kuma sanya shi cikin inuwarsa ranar da babu inuwa sai tasa, domin kuwa duk waɗannan al’amura suna daga cikin Rahmar Allah.

5. Dabi’ar tausayi a wajen bawa ita ce mafi girman hanyar samun rahmar Allah. Duk wani alheri na duniya da na lahira, Rahmar Allah sanadiyyarsa. Duk wanda ya rasa ɗabi’ar tausayi a zuciyarsa, to ya haramta wa kansa hanyar samun Rahmar Allah.

6. Bawa ba zai iya rayuwa ba sai tare da Rahmar Allah, ba zai iya wadatuwa ga barin ta ba daidai da ƙibtawar ido. Duk wata ni’ima da yake walwala a cikinta da kariya da yake samu daga duk wani abin ƙi, duka wannan bangare ne na Rahmar Allah.

7. Duk wanda yake son ya wanzar da ni’imar da yake ciki, ko ya samu ƙari a kan wadda yake da, to ya zamanto mai tausayi da jin ƙai ga al’umma. Allah ya sa mu dace.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button