Addini

Ramadaniyyat 1443 [12]Laƙanin Hangen-Nesa – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

1. Mutum mai hangen-nesa, shi ne mutumin da Allah (SWT) ya yi masa baiwar hashen sakamakon wani al’amarin tun gabanin faruwarsa. Jama’a suna girmama zancen mutane masu irin wannan baiwa ta hangen-nesa. Mutane sukan yi haba-haba da shawarwarinsu, domin dacewar da ake samu daga gare su.

2. Malam Ibnul Ҝayyim ya bayyana sirrin dacewa da wannan babbar baiwa ta hangen-nesa, inda ya tabbatar da cewa, kame idanu daga kallon haramun yana gadar wa bawa hangen nesa na gaskiya, wanda zai ba shi damar tantancewa tsakanin ƙarya da gaskiya.

3. Ya ambato wani bawan Allah mai suna Shah bn Shuja’ Al-Kirmani, wanda Allah (SWT) ya yi wa irin wannan baiwa ta hangen-nesa, yana cewa: “Duk wanda ya raya zahirinsa da bin sunna, ya kuma raya baɗininsa da sanya Allah a zuciya, ya kuma kame idanunsa daga kallon haramun, ya kuma hana zuciyarsa bin sha’awace-sha’awace, ya saba wa kansa cin halaliya, to wannan da wuya ne hangen nesansa ya zamanto kuskure”. [Duba, Abu Nu’aim, Hilyatul Auliya, juz’i na 10, shafi na 253].

5. Mal. Ibnul Ҝayyim ya ci gaba da bayyana cewa, da ma haka al’amarin Allah yake, yana yi wa bawa sakayya ne gwargwadon aikinsa. Duk wanda ya bar abu don Allah, sai Allah ya musanya masa da wanda ya fi shi alheri. Don haka idan mutum ya kame idanunsa daga kallon haramun, sai Allah (SWT) ya sakar masa hasken basirarsa, a madadin kame idanunsa da ya yi, sai kuma ya buɗe masa ƙofofin ilimi da imani da sanin Allah da hangen-nesa na gaskiya.

Wannan shi ne laƙanin wannan sirri. Allah ya sa mu dace. Amin.
[Duba, Ibnul Ҝayyim, Adda’u Wad-Dawa’, shafi na 417- 418].

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button