Labarai

Ramadan: Ku guji almubazzaranci ku kuma ci da mabuƙata — Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu hannu da shuni da ka da su yi almubazzaranci na abinci, sannan kuma su ciyar da talakawa mabuƙata.
Buhari ya yi wannan kira ne a saƙonsa na azumin watan Ramadan kamar yadda sauran shugabannin duniya su ka miƙa nasu saƙunan.
Buhari, a sanarwar da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitarfitar a jiya Juma’a a Abuja.
Majiyarmu ta samu wannan labari daga Daily Nigerian hausa a cewar Buhari, watan Ramadan wata ne da ya ke sanya wa idan an ji yunuwar azumi za a tuna yadda talaka ya ke fama da yunwa, inda ya ƙara da cewa hakan zai sa shugabanni su ji yadda wahalar yunwa ta ke.
Daga nan ne sai shugaban ƙasar ya shawarci al’umma da ka da su riƙa almubazzaranci da abinci da kuma kashe-kashen kuɗi na ba gaira ba dalili, inda ya yi kira da a riƙa taimaka wa maƙwabta da talakawa.
Ya kuma yi kira da a dage da addu’ar neman zaman lafiya a ƙasa da ma duniya baki daya, inda ya yi wa al’ummar Musulmi a faɗin duniya fatan kammala kwanaki 30 na Ramadan cikin koshin lafiya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button