MURNA TA KOMA CIKI:An Miƙa Bakin Balarabe Hannun Jami’an Tsaron Ƴansanda a Jihar Nasarawa
Akasin labari mai daɗi da jama’a suke dakon ji, ta sauya zane a halin yanzu dai an damƙa Bakin Balarabe hannun jami’an Ƴansanda a jihar Nasarawa.
Idan dai ba’a manta ba Bakin Balarabe ya damƙa Raƙumin shi ga sabon shugaban jam’iyya APC Abdullahi Adamu da niyyar tayashi murna, sai dai maimakon samun tukuici mai gwaɓi Bakin Balarabe ya samu tukuicin Naira Dubu Ɗari ne kaɗai, lamarin da baiyima Bakin Balarabe daɗi ba.
Wannan lamarin dai yasa ya sauya tunanin shi tare da cewa ya fasa bada wannan Raƙumin nashi ga Shugaban Jam’iyyar ta su.
Bakin Balarabe dai yayi tattaki ne da Raƙumin shi tun daga Katsina har zuwa Abuja wajen babban taron Jam’iyya domin karrama ita Jam’iyyar tashi ta APC yayin Convention.
Da muke zantawa da shi yace kuɗin da aka bashi ko kuɗin abincin Raƙumin basu kaiba balle kuma kuɗin Raƙumin kanshi da sauran ɗawainiyar da yayi tun daga Katsina har zuwa Abuja kafin kuma daga nan ya yanki hanya zuwa Nasarawa.
Ibrahim yace Shugaban jam’iyyar ya bashi dubu ɗari da umarnin cewa a ɗauki Raƙumin akai shi Gidan Gona yayin da shi kuma ya kama hanyar zuwa Abuja, sai dai Ibrahim yace hakan bata saɓu ba dan haka yayi yunƙurin tafiya da Raƙumin shi yayinda su kuma yaran shugaban jam’iyyar suka ce lallai hakan kuma ba zata yiyu ba.
Ya zuwa yanzu dai lambar wayar Bakin Balarabe idan an kira tana ta kaɗawa amma ba’a ɗauka.
Muna mashi fatan samun mafita akan wannan lamarin.
–Katsina City News