Addini

Mun Aika Malamai Tafsirin Ramadaan A Sama Da Masallatai Dubu Goma – Sheikh Bala Lau

Ash Sheikh balau yayi kira ga malamai su dage da yiwa kasa addu’a, mawadata su taimakawa mabukata

Shugabana kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah, Ash-Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa kungiyar ta tura malamai Tafsiri a wata mai al-farma na Ramadaan zuwa masallatai sama da dubu goma a ciki da wajen Nijeriya.

Shehin malamin ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da khuduban jumma’a a masallacin jumma’a na hedikwatar kungiyar.
Idan ba’a manta ba dai, a makon da ta gabata ne dai kungiyar ta fitar da jadawalin malaman da ta tura Tafsiri a jihohin Nijeriya. Bugu da kari, tura malaman bai tsaya a Nijeriya kadai ba, hard a kasashe musamman yammacin Afirka da kuma kasashen turawa inda kungiyoyin ahlusunnah suke, wadanda a shekarun baya shugaban ya ziyarta.
Bala Lau ya kuma yi kira ga malaman da kungiyar ta tura Tafsiri da su mayar da akalan karatun su wajen karantar da addini yanda Manzon Allah SAW yayi, tare kuma da yiwa kasa addu’a. “Hakika wannan kasa babu shakka ana cikin wani hali. Amma mafita tana wurin Allah. Wannan yasa muke kiran malamai da aka tura tafsiri das u cigaba da yiwa kasa addu’a’’’inji shi.

Malamin ya kuma yi tsokaci akan halin rashin tsaro da ake fama das hi,inda yace “a lokaci da ake ciki na fasahar zamani (technology) bai kamata ba a ce an samu ‘yan ta’adda su ci karen su babu babbaka ba, har su tare jirgin kasa su kasha na kashewa kuma su kwashe na kwashewa. Saboda haka ina ministan sadarwa, ina shugabannin tsaro, ina shugaban kasa, hakika akwai bukatan kara kaimi wajen yaki da ta’addanci a kasar nan’’.

Da yake Magana akan watan Ramadaan, malamin yayi kira ga manyan ‘yan kasuwa, attajirai da shugabanni da cewa su bude taskokin su saboda al’umma, musamman yanzu da ake cikin yanayi na tsadan rayuwa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button