Labarai

Mubarak Bala ya amsa laifin aikata saɓo a gaban kotu

Mubarak bala wanda ya wallafa sakonin cin mutuncin addinin Musulunci wanda a shekarar abun ya dauki duk musulmin duniya inda yake cewa

“Musulmi zasu fara azumi,ga Ubangijin da ya ƙi yaye musu talauci duk da salloli 17 da suke yi kulla yaumin

Ina ma ace akwai Allah”

 

Wannan kalamai na cin mutuncin Addinin da kore babu Allah ya sanya yan uwa musulmi sunka shiga farautarsa har anka kurfanar da shi to shine a yau anka ci gaba da sauraren ƙararsa ga abinda Bbchausa na ruwaito.

 

Wata babbar kotu a Kano da ke arewacin Najeriya ta sake aike wa da Mubakar Bala zuwa gidan gyaran hali, saboda ci gaba da tsare rayuwarsa da kuma gazawar lauyoyinsa na gabatar wa kotun da cikakaken takardun da za su tabbatar mata cewar yana fama da rashin lafiya.

 

An karanto wa Mubarak Bala caji 14 da ake tuhumarsa a kai na yin sabo.

 

Yayin zaman kotun, an karanto masa sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook, wadanda ya yi kalaman batanci ga addinin Musulunci.

 

Ya amsa dukkan caji 14 da aka karanto masa da cewar ya aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.

Mubarak Bala ya amsa laifin aikata saɓo a gaban kotu
Mubarak Bala ya amsa laifin aikata saɓo a gaban kotu

Ganin haka sai lauyansa ya roki kotun ta ba shi damar ganawa da wanda yake wakiltar, wato Mubarak Bala, kuma bayan ta amince, ya yi kokarin nuna ma sa tasirin cewa ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa.

Amma bayan da lauyan ya sanar da kotun cewa Mubarak Bala na son sauya amsar da ya bayar a gaban kotun, sai alkalin ya sake tambayar wanda ake tuhumar ko haka lamarin yake.

 

Mubarak Bala ya sanar da kotun cewa ba zai sauya amsa laifinsa da ya yi a gaban kotun ba.

 

Alkali kotun ya tambaye shi ko ya fahimci nauyin abubuwan da yake cewa, kuma wanda ake tuhumar ya amsa cewa ya fahimci komai.

 

Ya kara da cewa babu wanda ya tursasa masa don ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa. Sannan ya ce babu wanda yayi masa wani alkawari, ko ya sanya masa wani ra’ayi, sai dai ya bukaci kotun ta yi masa sassauci da kuma adalci.

 

Wakilin BBC da ke kotun ya ce kotun na ci gaba da sauraron shari’ar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button