Kannywood

Mai neman suna Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka

Jaruma Nafisa Abdullahi ta yi martani mai zafi ga Sarkin Waka kan wallafar da yayi na kare iyayen da ke haihuwar yara su barsu suna almajiranci Jarumar ta kira Naziru Sarkin Waka da mai neman suna, ta kara da cewa ta san matsalarsa kuma idan ya isa, ya bugi kirji ya kira suna ne A cikin makon nan ne Nafisa ta caccaki iyaye da ke haihuwar yara babu kulawa suna sakinsu a titi inda suke zama almajirai legit na ruwaito

Kwatsam sai ga wallafar Sarkin Waka inda yake bayyana cewa ba almajirai bane yaran da iyayensu suka haifa suka kasa kula da su ba, idan kana son ganin ‘ya’yan da iyayensu suka haifa kuma suka kasa kula dasu, toh ka taho masana’antar fim.

Jaruma Nafisa Abdullahi bata yi kasa a guiwa ba taje shafinta na Twitter inda ta yi wa mawakin martani inda ta kira shi da mai neman suna. Idan kuma ya isa, ya bugi kirji ya kira suna.

Mai neman suna!!! Ka bugi kirji ka kira suna mana. Duk da dai na san matsalarka. Ramadan Kareem.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button