Labarai

Kungiyar ta’addanci ta Ansaru sunyi rabon kayan azumi a Jahohin kaduna,katsina da Zamfara

A yanzu nan majiyarmu ta samu wani labari daga wani fitaccen marubuci a kafar sada zumunta Aliyu Samba akan cewa wata sabuwa kungiya mai irin kayan irin na mutanen Pakistan sun bayyana a arewacin Nigeriya harda rabon kayan azumi.Kungiyar ta'addanci ta Ansaru sunyi rabon kayan azumi a Jahohin kaduna,katsina da Zamfara

Kungiyar ta’addanci ta Ansaru sun yi rabon kayan Azumi a ƙauyukan Jihohin Katsina, Zamfara da kuma Kaduna. Ƙauyukan sun hada da Kwasa-kwasa, Kuyallo, Shado, Gwandu, Farin Batu, Layin Ɗan Auta, Kwanar Adua, Jabi, Saminaka, Nacibi, Kwadaga, da kuma Shado.

Wani manomi ya sheda cewa yan kungiyar sun ce da shugabannin yan bindiga (Baushe wanda siriki ne ga Dogo Gide da Musa Shado) su bar wannan yankunan da suke nan take. Kungiyar na ta ƙoƙarin samun alaka mai ƙarfi da al’ummomin ƙauyukan da aka ambata a sama.

Suna sanya kayan irin na mutanen Pakistan (Ruwan Toka) tare da riga ta kakin soja.

Mallam Abba, wanda shugaba ne ga yan kungiyar ta’addanci ta Ansaru na cigaba da fadada ayyukan sa na shigo da mutane cikin kungiyar su, a yanzu haka ya fadada aikin sa da fara jawo mata a yankin Kankara zuwa kungiyar Ansaru. Wata majiya ta bayyana cewa mata da matasa da dama na shiga cikin wannan kungiyar a garuruwan Katsina da kuma Kaduna. 

~Edrees4P

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button