Labarai

Kotu ta daure Mubarak Bala shekara 24 a gidan yari kan aikata saɓo Da kore babu Allah

Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke wa Mubarak Bala hukuncin shekara 24 a gidan yari kan laifin ɓatanci ga addinin Islama.

An yanke masa hukunci ne kan laifuka 18 da aka zarge shi ciki har da amsa laifin aikata saɓo da ya yi a gaban kotu.

Sai dai ya shaida wa kotun cewa lokacin da ya yi rubutu bai san cewar saƙon zai iya haifar da tashin hankali ba, sannan kuma hakan ya zama darasi a gare shi, nan gaba.Bbchausa na ruwaito

An kama Mubarak Bala, shugaban kungiyar waɗanda ba su yarda da addini ba ta Najeriya, a ranar 28 ga watan 2020 a gidansa da ke jihar Kaduna.

Sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu a Kano bisa zargin aikata sabo ta hanyar wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook.

Sakon da ya wallafa ya fusata al’ummar Musulmai a Najeriya.

Laifin da Mubarak Bala ya aikata
Tun a watan Afrilun 2020 ne aka zargi Mubarak Bala da cin zarafin addinin Musulunci a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Wata tawagar lauyoyi ce ta miƙa wa ‘yan sanda ƙorafi a Jihar Kano inda su kuma ƴan sandan Jihar Kaduna suka kama Mubarak suka mayar da shi Kano jiharsa ta haihuwa, inda a can ne dimbin Musulamai suka rubuta wa hukumomi korafi da zarginsa da yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

A lokacin wasu masu rajin kare hakki sun yi ca a shafukansu na zumunta suna neman a saki Mubarak Bala, wadanda suka ce yana da ‘yancin shiga addinin da ya kwanta masa a rai.

Barista Salisu Salisu Umar ne jagoran lauyoyin da suka yi ƙorafi kan Mubarak, kuma tun farko ya faɗa wa BBC cewa ba don ya bar addinin Musulunci suka nemi a kama shi ba.

“Mun yi musu ƙorafi ne kan aibata Annabi S.A.W. da ya yi a shafinsa na Facebook,” a cewar Salisu Salisu.

Ya ci gaba da cewa: “Ba wai don ya yi ridda ba ne ko sabo, korafinmu a kan barin masu addini su yi addini ne.”

“Abin da muke nufi shi ne, tun da shi (Mubarak Bala) ya bar Musulunci tun a shekarar 2014 bai kamata kuma ya rika aibata addinin ba da kuma abin da masu binsa suka yi imani da shi.

“A matsayinmu na lauyoyi, daga cikin hakkinmu mun nemi ‘yan sanda su binciki abin da yake fada ko ya saba da abin da aka iyakancewa mutum ya yi magana kan addini.”

Barista Salisu ya bayyana cewa suna so ne a hukunta shi da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button