Labarai

Ko akwatin zaɓensa ba ya iya ci ballantana zaɓen shugaban ƙasa, APC ta caccaki Osinbajo

Jam’iyar APC, reshen Jihar Legas ta caccaki Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo a kan baiyana takarar sa ta shugaban kasa da ya yi a jiya Litinin.

Mai magana da yawun jam’iyyar ta APC a Legas, Seye Oladejo, ya soki mataimakin shugaban kasar ne a wata sanarwa da ya fitar a juya Litinin.

Jaridar daily Nigeria hausa ta rawaito cewa a wata sanarwa da ya fitar a jiyan, Oladejo ya bayyana cewa Osinbajo ya na da dama a matsayinsa na ɗan ƙasa ya fito takara, inda ya ƙara da cewa sai ya nuna ba zai ci zaɓen ba.

Kakakin jam’iyyar ya baiyana cewa sun san da take-taken Osinbajo cewa zai tsaya takara, inda ya ce abin da su ke bukata shi ne ƴan siyasa su hadu a wajen zaɓen fidda gwani.

A cewar sa, da ya kalli bidiyon da Osinbajo ya ƙaddamar da takarar ta sa a cikin daki, bai fahimci jawabin tsayawa takara ya ke yi ba.

Rahoton ya ce Oladejo ya na ganin kwararren ‘dan siyasa APC ta ke bukatar ta tsaida, ya na nuni ga Tinubu.

“Babu matsala. Mun san cewa zai ayyana niyyar takara. Su kyale mu ayi zaben fitar da gwani. Ya zo, ya (Osinbajo) gwabza da Asiwaju (Bola Tinubu).”

“Sam ban damu ba. Mun fahimci ya na da damar da zai yi takara a tsarin mulkin kasa. Mun lura da yadda ya gagara yin abin kirki a shekaru takwas.

“Na yi tunanin makoki nake sauraro, sai can gane cewa jawabin tsayawa takara ne a cikin daki. ‘Yan Najeriya za su yi masa hisabi idan lokaci ya zo.

“Iya sani na, mataimakin shugaban kasa ne yake kula da tattalin arzikin Najeriya.

“Abin da kurum mu ke bukata shi ne ayi zaben fitar da gwani. Sai mu ga irin goyon bayan da Osinbajo zai samu daga ‘ya ‘yan jam’iyya (APC).

“Wannan mutumin ne da ya gagara lashe akwatin zabensa. Bani da wani labarin cewa abubuwa sun canza daga zaben da aka yi karshe zuwa yanzu,” in ji shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button