Kannywood

Kahutu Rarara ya yi kaca-kaca da gwamnatin Shugaba Buhari, a cikin sabuwar wakarsa

Shahararren mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara, wanda ya yi fice wajen wakokin girmama shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan ‘yan siyasar Arewa, ya yi tsokaci kan abin da ya dauka na gazawar gwamnati mai ci a wata sabuwar waka jaridar dimokuraɗiyyar ta ruwaito

A cikin wakar ya jagoranci gungun wasu fitattun mawakan Hausa karkashin kungiyar Kannywood ta 13-13.

Bayan wata 5, Rarara bai saki wakar da ya ce Masoya Buhari zasu dauki dauyin ta ba.

Sai dai wannan sabuwar Waka ta haifar da cece-kuce a kan ko mai goyon bayan Buhari ba ya tare da shi ne a yanzu?

Labarin sabuwar wakar ya yadu ne yayin da mai magana da yawunsa Rabi’u Garba Gaya ya wallafa ta a shafinsa na Facebook.

A farkon shekarar da ta gabata ne mawakin Buhari ya fara wani yunkuri na neman ‘yan Najeriya su dauki nauyin albam dinsa na gaba (wakar garaya) ta hanyar turamasa kudi Naira 1000 kowanne.

Mawakin ya ce yana son jama’a su dauki nauyin wakar da za ta nuna irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu.

Tun bayan da ya fitar da wannan sanarwar a bainar jama’a, magoya bayansa ke dakon fitowar wakar domin an ce an samu miliyoyin Nairori.

Sai dai wasu sun yi Allah wadai da bukatar mawakin, inda suka bayyana ta a matsayin yaudara yayin da wasu suka lashi takobin cewa ba zai yi komai ba wajan yin wakar da aka yi niyya.

Wani abin ban mamaki, masoyan mawakin sun yi mamakin yadda mawakin maimakon wakar yabo ga Buhari, ya rera wakar rashin tsaro.

A cewar masana, a cikin wakar, an soki Buhari da “kasar nan” da kuma alkawarinsa na kare rayuka da dukiyoyi.

Wani jigo a cikin baitocin wakokin ya kasance kamar haka

, “Mutane kalilan ne a yanzu suke tunani, rashin tsaro ya karu a garuruwa da kauyuka. Abin da ya fara a matsayin ji ya zama gaskiya. Burinmu shi ne mu ga cewa mun mayar da al’amura a kan hanya”.

Wadanda suka fito a wakokin sun hada da Aminu Ladan Ala, Nura M Inuwa, Ali Isa Jita, da sauran fitattun mawakan Hausa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button