Labarai

Ka Fito Takarar Shugaban Kasa Gwamna Zulum ko kotu ce zata Rabamu da kai – Murjanatu Diri

wata matashiya mai suna Murjanatu Diri dalibar ilimin kiwon lafiya da ke karatu a jami’ar  birnin kebbi da take karatun microbiology tayi kira ga Gwamna Farfesa Babagana umara zulum da yayiwa Allah ya fito takarar shugaban kasar Nigeriya a zabe mai zuwa 2023.

Murjanatu Diri tayi wannan kira ne duba da irin yadda wannan bawan Allah yake kokari sosai wajen kwatanta gaskiya da adalci ga mutanen jihar borno.

Ka Fito Takarar Shugaban Kasa Gwamna Zulum ko kotu ce zata Rabamu da kai  - Murjanatu Diri
Murjanatu Diri

Ta kara da cewa Farfesa zulum shine mutum da Nigeria take buƙatarsa a yanzu duba da rashin tsaro da kuncin rayuwa da yayiwa al’umma katutu a ƙasar nan.

Saboda haka na yanke shawara idan bai fito ba to kotu ce zata rabamu da shi.

Miye shawarku yan uwa?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button