Kannywood

Jaruman kannywood sunyiwa Sarkin waka dawafi akan Kalamansa ga kannywood

Tsugunne bata kare ba dangane da rigimar Sarkin Waka da Nafisat Abdullahi, yayin da maganganu suke ta bullowa ko ta ina, labarunhausa ta ruwaito.

Wasu daga cikin ‘yan fim din sun goya masa baya yayin da wasu suka dinga caccakarsa musamman a Facebook da TikTok.

Yawancin wadanda suka je Saudiyya yin Ummara sun yi shiru ba tare da sun tofa komai ba ko kuma yin martani akan maganimun da ya yi.

Jarumi Malam Ibrahim Sharukhan, Suleiman Costome, mai haska dandali, Sani Candy da kuma Jarumi Adebo duk sun bayyana cewa sun yi dawafi inda suka kai kukansu ga Allah akan munanan maganganun da Sarkin Waka ya yi

A cewarsu, sun yi dawafi inda suka kai karar Naziru wurin Allah akan ya yi musu sakayya da kuma maganganun da ya ke yi akan masana’antarsu.

Jarumi Malam Ibrahim Sharukhan ya fara da cewa:

Da kai nake, wallahi a Makkah muke, garin ma’aiki muke, Allah ya kara wa Annabi daraja ya bar mu da soyayyarsa.

“Wallahi mun yi dawafi akanka kuma mun hada ka da Allah, kuma mun bar ka da shi. Allah ya yi mana sakayya.”

Daga nan Suleiman Costume ya ce:

Ni babu abinda zan ce akanshi sai dai in ce mun bar shi da Allah.”

Ya ci gaba da cewa sana’arsu ita ce mutuncinsu don haka sun kai kara wurin Allah, Allah ya yi musu sakayya akan maganganun da ya yi akansu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button