Kannywood

Iyayen Fati Muhammad ne suka raba mu, Tsohon mijin Jarumar, Sani Mai Iska

Sani Musa Haladu wanda aka fi sani da Sani Mai Iska, tsohon mijin tsohuwar jaruma Fati Muhammad wacce tauraronta ya haska a shekarun baya da suka shude ya bayyana silar rabuwar aurensu.

A wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da shi cikin shirinta na Daga Bakin Mai Ita, ya yi bayani akan alakarsa da tsohuwar matarsa tun daga haduwarsu har rabuwar.

sani mai air

Ya fara da gabatar da kansa inda ya ce an haife shi a garin Kano a Unguwar Gwammaja. Kuma ya fara ne da karatun addinin musulunci.

Ya bayyana yadda ta fara harkar fina-finai inda ya ce yana da abokai masu wasannin al’adun gargajiya kuma ya fara fim a 1998.

A cewarsa, ba Fati Muhammad kadai ya aura ba, ya taba auren wata jaruma Wasila, amma yanzu ta rasu kuma suna da diya daya da ita.

Ya ce sun kulla alakar aure da Fati Muhammad tun daga wani fim da suka tafi mai suna Sakamako, kuma ta bar sarkoki da sauran muhimman abubuwa a hannunsa. Da ga nan suka fara soyayya.jaridar labarunhausa ta tattara bayyanai

A cewarsa Marigayiya Hajiya Amina ce ta karfafa alakar soyayyar tasu. Sannan Ali Nuhu ma ya yi kokari sosai akan aurensu.

 

Yayin da aka tambayeshi batun tafiyarsu Ingila tare da Fati Muhammad, ya kada baki ya ce:

“Shekara ta 2002, lokacin za ayi World Cup, sai DFID da USAID, suka zo za su yi tallace-tallace da wayar da kai akan HIV/AIDS sai suka zabi kudu da arewa.

“Sai ya zama a arewa sunan Fati Muhammad ne ya fito kuma lokacin mun yi aure da ‘yan watanni. Sai aka same ni aka yi min magana akan cewa za ayi tallar kuma ba a Najeriya za ayi ba, ko dai a Afirka ta kudu ko kuma UK, shi ne silar tafiyarmu.”

Ya ci gaba da cewa kwana 7 kadai suka yi, daga baya ya koma saboda wasu dalilai. Daga baya ya bukaci ta bi shi kuma ta bi shi wanda suka kwashe shekaru 3 daga baya suka samu matsala.

Da aka tambaye shi dalilin rabuwarsu ya ce:

“Gaskiya tana da gaskiya ina da gaskiya. Saboda dalilinta a lokacin mahaifiyarta da mahaifinta, Allah ya ji kan su don duk yanzu sun rasu.

“Ni kuma dalilina a lokacin ban gama senior Secondary School ba na samu dama ba zan so in saki ba don na yi nisa. Ita kuma tana matukar kaunar mahaifiyarta.”

Ya daga nan ne suka nemi rabuwa wacce sai da suka dawo Najeriya sannan ya yi mata saki daya, sai dai ita ta ce saki uku ne kuma a haka suka tafi.

Da aka tambayeshi idan zai yiwu ya mayar da ita ya ce ai ba zai yiwu ba saboda a wurinta saki uku ne. Amma a cewarsa kaddara ce kawai ta raba su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button