Labarai

Ina Matukar Son Gwamna Ganduje, Kuma Inason Ya Aure Ni ~ Surayya Muhammad Maigari

Idan baku manta ba a shekarar da ta gabata jaridar “Daily News Hausa” matashiya Surayya Muhammad Maigari, ta bayyana irin so da kauna da take yiwa Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda hakan ya jawo cece-kuce a kafofin sadarwar zamani.

Al-umma da dama sun ta tofa Albarkacin bakinsu akan kudurin matashiyar, haka zalika a yau Laraba matashiyar ta sake bayyana kudurinta tare jan kunnen masu kiranta suna mata barazana.

Ga sakon da matashiyar ta bayyana a shafinta na Facebook kamar haka; “Saboda nace inason mai girma governor Ganduje shiyasa wasu mutane suke kirana da Private Number a suna min barazana toh duk wanda yasan ya isa ko ta isa ya bude layinsa ko kuma tabude layinta ta kirani, kuma har yanzu una kan bakana na cewa inason Governor Ganduje ni daku duk wanda ya fasa bai san Allah”.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button