Labarai

Idan ‘yan Nijeriya sunka yi sakaci Buhari zai cigaba da mulkinsu har abada – Sule lamido

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya Alhaji Sule Lamido ya ce “ƴan Najeriya idan sun ga dama su bar Buhari ya tabbata a mulki har a bada.”

Ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa a kwanakin baya.

Tsohon gwamnan ya kuma ce “jam’iyyar APC annoba ce a Najeriya, ta kawo masifa marar iyaka, gyaran barnar APC nan gaba aiki ne babba, tun da yake ta kawo gaba tsakanin ɗa da uwa, da tsakanin wa da ƙani da tsakanin gari da gari, dangi da dangi, addini da addini da kudu da arewa.”

Amma duk inda ake son mu bayar da gudunmowa za mu bayar wallahi,” a cewarsa.

BBC Hausa ta tuntuɓi mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya Garba Shehu don jin ko za su mayar da martani, amma ya ce yanzu ba ta tasa suke ba, sai daga baya za su yi martani.

Sule Lamido ya ce saboda kaunar Buhari da ƴan Najeriya suka so ya yi mulki “an ce mana arne, an ce mana kirista, an ce ba ma son Musulunci, ba ma son arewa, komai an yi, an ma ce mu da ƴaƴanmu ɓarayi ne.

An ce Buhari waliyyi ne, ma’asumi ne, kaza-kaza duk an yi, an ɓata mu.”

Ya ce “idan dai har yanzu ƴan Najeriya ba su dawo rakiyar APC ba to sai su tabbatar da Buhari ya yi ta mulki har abada.”

“Tun da suna ganin ya kyauta, to duk mu taru mu ce Buhari don Allah ya ci gaba da mulki har abada.”

Jigon na babbar jam’iyyar adawar ƙasar ta PDP dai ya yi zargin cewa APC mai mulki ta rusa dukkan ginshiƙan da aka gina ƙasar a kai don tabbatar da haɓakarta.

A cewarsa, hakan ta sa PDP ta duƙufa don ganin ta karɓe mulki da kuma sake lale da nufin ceto Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido na cikin mutanen farko da aka kafa PDP da su tun 1998, kuma a tattaunawarsu da Ibrahim Isa ya ce PDP ce kaɗai za ta fitar da Najeriya daga ƙangin da take ciki.

Ga dai cikakkiyar hirar a ƙasa sai ku latsa ku saurara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button