Labarai
Hausa ta Shiga Sahun Harsunan Fassara Hudubar Masallacin Madina
Advertisment
Hukumomin Masallacin Annabi
Muhammad (S.A.W) da ke Madina a kasar Saudiyya, sun sanar da harshen Hausa a cikin harsuna 10 da za a rika amfani da su wajen fassara hudubar sallar Juma’a.
Hakan dai na nufin Hausa ne kadai harshen da ya samu damar shiga jerin harsunan.
Sanarwar ya fito ne ranar Juma’a, kamar yadda kafafen yada labaran Saudiyya suka rawaito.
Advertisment
Ga jerin harsunan:
1.English
2.Urdu
3.French
4.Bengali
5.Malay
6.Turkish
7.Hausa
8.Chinese
9.Russian
10. Persian