Harin Ta’addanci: An buƙaci Buhari daya sauke El-Rufa’i, ya sanya Dokar ta ɓaci a Kaduna
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari an buƙace shi daya cire Gwamna Nasir El-Rufa’i a matsayin Gwamnan Jahar Kaduna tare da ayyyana Dokar ta ɓaci a Jahar ba tare da ɓata Lokaci ba.
Tsohon Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan kuma mai Fashin baƙi na Siyasa Reno Omokri ya bada shawarar, yana mai cewa Buhari yana lalata yankin Kudu Maso Gabas ba tare da tunanin cewa wannan bama-bamai da aka sanyawa Jirgin Ƙasa ya taɓa yankin ba.jaridar dimokuraɗiyyar ta ruwaito
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana irin alhinin sa na yadda Mutane Ƴan Ƙungiyar IPOB suka kashe su, kafin daga bisani Gwamnati mai ci a yanzu ta aike da Sojoji ga yankin Kudu maso Gabas ta janyo matsaloli da dama.
Ya kuma bayyana irin kokwanto na yadda Buhari ya Kasa sanya Mulkin Soji a Jahar Kaduna, yana mai cewa Ƴan ta’addan zasu iya fasawa Buhari da El-Rufa’i Asiri.
Jahar Kaduna ta kasance tana fama da matsalar tsaro wanda suka tashi daga garkuwa da mutane zuwa kashe Ɗalibai, kai hari ga Wurin Sojoji, zuwa cigaba da kai hari ga da ƙwace ƙauyuka a jahar, gami da kai hari a Filayen Jiragen Sama dana Ƙasa da wuraren Gwamnati.
Ƴan ta’addan a ƴan kwanakin nan sun tada bam a hanyar Jirgin Ƙasa ta Abuja-Kaduna tsakanin Katari zuwa Rigina, tare da kashe Fasinjoji gami da sace mutane da dama.