Labarai

Gwamna Bala Ya Rabawa Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Bauchi Da Hakimanta Motoci

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a yau Alhamis ya gabatar da sabbin motoci ga shugabannin kananan hukumomi da Hakimai.Gwamna Bala Ya Rabawa Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Bauchi Da Hakimanta Motoci

A yayin rabon mitocin, wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar Bauchi, Gwamna Bala ya bayyana cewa an raba motocin ne bisa bukatar da Mai Martaba Sarkin Bauchi ya gabatar na cewa a taimakawa Sarakunan Gargajiya da ababen hawa.

Kamar yadda Gwamna Bala ya ce, motocin da aka raba, an bada su ne domin yabawa da irin sadaukarwa da wadanda suka amfana da motoci suka yi wajen cigaban jihar.

Gwamnan ya yi kira ga Hakiman da su taimakawa gwamnatinsa wajen bunkasa harkokin ilmi, lafiya, tsaro da sauransu domin cigaban jihar baki daya.

A yayin nasa martanin, Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaimanu Adamu ya yabawa Gwamna Bala bisa hidimar da ya yi, inda ya tabbatar masa da cewa za su cigaba da baiwa gwamnatinsa goyon baya don ganin ta cigaba da samun nasara.

Bikin gabatar da motocin ya samu halartar mataimakin Gwamna, Sanata Baba Tela, Sakataren Gwamnati, Shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Sarakunan, Bauchi, Katagum, Misau, Ningi, Jama’are, Dass da sauransu.

Daga Lawal Mu’azu Bauchi
Mai taimakawa Gwamnan Bauchi
Kan harkokin sabbin kafafun sadarwa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button