EFCC ta kama ɗaya daga cikin gungun ƴan damfara da su ka damfari Sarkin Okuta N33m
Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Ƙasa, EFCC, shiyyar Ilorin, ta kama wani matashi mai suna Fidelis Poor, wanda ake zargi da haɗa baki da damfarar wani basarake mai daraja ta ɗaya a Jihar Kwara, Idris Sero Abubakar, maƙudan kuɗaɗe har N33,399,999.00. .
Fidelis, mai shekaru 30, wanda ya fito daga Stwue a karamar hukumar Konshisha ta jihar Binuwai, tare da wasu wadanda ake zargi kuma su ka tsere, sun haɗa baki ne da zambatar sarkin kan cewa ya na da kwantena kayan da za a yi amfani da su wajen ayyukan ci gaban Okuta kuma ana daf da biyan kuɗin fiton kayan a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Abubakar, wanda shi ne Sarkin Okuta a Ƙaramar Hukumar Baruten, tsohon dan majalisar wakilai ne.
A cikin ƙarar da ya shigar, mai dauke da kwanan watan Nuwamba 30, 2021, Sarkin ya yi zargin cewa gungun ‘yan damfarar ne ya kira shi ta wayar tarho a wani lokaci a shekarar da ta gabata cewa yana da kwantena da zai fitar da ita a Abuja kuma ya bukaci a ba shi adadin kudin domin ya biya kuɗin fito.
Sarkin ya bayyana cewa ƴan damfarar sun bashi asusu daban-daban, inda ɗaya da ga cikin su na ɗauke da sunan Fidelis Poor domin ya saka kudin.
A cewarsa, ƴan damfarar daga baya sun nemi ya kira wani “Mai bishara Rose Marry Oni (JP)” don karɓar kwantenar kayan.
Ya kuma bayyana cewa kokarin da aka yi na kai kayan ko kuma dawo da kudadensa bai yi nasara ba, don haka ya kai kara EFCC.
A cewar sa, bayan da hukumar ta karɓi ƙorafin nasa, sai ta fara binciken ƙwaƙwaf, wanda ya kai ga damƙe shi Fidelis ɗin.
Za a gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da ake ci gaba da kokarin kama sauran ƴan gungun da su ka ranta a na kare.