Daga fara tafsirin Malam Kabiru Gombe daga biyu ga Ramadan zuwa jiya an tara kudin gudumawar marayu milyan 32
Masha Allah wannan abun yayi sha’awa sosai wanda ya kamata a yabawa mutanen da sunka taimakawa waɗannan mutane tare da shehin malami Sheikh kabiru haruna Gombe da alaramma Sheikh Ahmad suleman kano akan assasa wannan gidauniya.
Wani bawan Allah mai suna Adam Muhammad a shafinsa na sada zumunta ya wallafa wannan bayyani.
“An sayi kayan abinci, turamen zani, da shaddoji an rabawa marayu a helkwatar Izalah tare da baiwa kowanne 5k kudin dinki.
Sannan an dauki nauyin karatun marayu yara 100. An dauki nauyin aurar da ‘yan mata marayu guda 20, kowacce za a kashe mata 300k wurin mata kayan daki, sannan za a koya musu sana’a.
A wannan hidimar an kashe wadannan kudaden har sai da Sheik Bala Lau yayi cikon milyan biyu.
A gudumawar da aka tara yau an samu sama da milyan daya.”