Addini

Da na daina fadin gaskiya a matsayin liman gara na koma dako – Sheikh Nuru Khalid

Shiekh Nuru Khalid ya mayar da martani kan dakatar da shi daga limanci da kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ƴan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja ya yi masa a masallacin sakamakon hudubarsa ta ranar Juma’a da ta tayar da ƙura a Najeriya.

A hirarsa da BBC malamin ya ce gaskiya ce ya fada a hudubarsa ta Juma’a kuma bai yi nadama ba.

“Idan suka ce na daina faɗin gaskiya a Najeriya, na daina cewa a daina kashe mutane, to gara na yi dako ya fi mun limanci,” in ji Shiekh Nuru Khalid

Kwamitin Masallacin ƙarƙashin jagorancin Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau ya ce ya dakatar da malamin ne daga Limanci saboda hudubarsa ta tunzura jama’a.

Ga bidiyon nan kasa.

“An ɗauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma’a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai ‘yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi.”

Amma a martaninsa Sheikh Nuru Khalid ya ce ya yi mamakin mutumin da ya fito daga Zamfara, jihar da har yanzu babu zaman lafiya zai fito ya ce ya dakatar da shi saboda ya yi wa’azi kan hana kashe al’umma

Mataimakin shugaban kwamitin Masallacin ɗan Neja ne amma ba ya iya zuwa yankinsu,” in ji Sheikh Khalid.

Ya ƙara da cewa: “su suke taya mu faɗa ba, yanzu ne don an yi maganar a kawo tsaro ya zama barazana?”

Malamin ya ce zai ci gaba da hudubarsa, “Wai ace kada muyi magana a kan matsalar tsaron ƙasar nan ba ta taso ba,” in ji Malamin.

Ya ce ba zai ce ba zai koma limanci ba idan sun nemi shi, amma ya danganta da yadda suka nemi shi.

Idan sun nemi a matsayin liman mai mutunci, wanda idan za a ba shi shawara za a mutunta shi a kira shi a bashi shawara, “to zan dawo.”

“Amma idan suka zo suka ce sai na daina daina fadin gaskiya kan kashe kashen al’umma, to gara na yi dako ya fi mun na zama liman.”

Sheikh Nuru Khalid ya sha caccakar gwamnati kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, kuma hudubarsa na zuwa ne bayan harin da ƴan bindiga suka kai wa jirgin ƙasa a ranar Litinin inda aka kashe mutum takwas tare da sace mutane da dama.

A cikin huɗubar Malamin ya ambaci wani da ke cewa “harakar tsaro ta zama kasuwanci a Najeriya, jinin talaka ya zama kayan kamfen a kasar nan, sai zaɓe ya kusa kashe kashe zai karu.”

“Mun dade muna hakuri – hanya ba kyau, talauci mun hakura, tsadar rayuwa mun hakura, karya mun hakura, kwashe kudin kasa mun hakura, ku bar mu mu zauna da ranmu kuma ba zai yiyu ba?”

Don haka a cewar Malamin abin da ya kamata talakan Najeriya ya yi shi ne ya ƙauracewa zaɓe har sai an daina kashe rayukan al’umma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button