Burina daya tak yanzu! Na auri Dr Rabi’u Musa Kwankwaso – Moofy
Babbar Mawakiyar Hausa da Turanci kuma mai fassara Fina-finan Indiya zuwa Hausa da Muryoyi daban-daban Mufida wacce akafi sani da Moofy tace yanzu Burin ta daya tak a Duniya shine ta Auri Tsohon Gwamnan Kano Kuma Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Moofy ta bayyana hakane yau Lahadi 10/4/2022 a shafin ta na sada zumunta facebook, inda Al’ummah da dama suke Tofa Albarkacin bakinsu.
Daga ɗaya cikin masoyan Dr Rabiu Musa Kwankwaso Khadijah Garba sanusi itace ta fitar da wannan farin jini da shugaban jagoransu ya samu irin yadda matashi mai jini a jikan ta nuna burinta a duniya ta malake shi.
Ba kasa fai yan siyasa suke samun irin yadda yan mata da zawarawa ke nuna sun bada kansu agaresu ba na nuna cewa idan sunka samesu a sun cika burinsu na duniya.