Labarai

Buhari ya ci amanar ƴan Najeriya – Naja’atu Muhammad

Fitacciyar ƴar siyasar nan kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Hajiya Naja’atu Mohammed ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ci amanar ƴan Najeriya musamman al’ummar arewa da su ka zaɓe shi da nufin ya yaƙi cin hanci da rashawa da ya addabi ƙasar.

Hajiya Naja’atu Muhammad wacce tana ɗaya daga cikin waɗanda suka riƙa tallata Muhammadu Buhari a zaben 2015 ta bayyana hakan ne a yau Talata lokacin da ta ke tsokaci akan afuwar da fadar shugaban ƙasa ta yiwa gwamnonin jihohin Plateau da Taraba.

Idan za a iya tunawa dai a makon jiya ne Labarai24 ta rawaito cewa majalisar koli ƙarƙashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da matakin yiwa wasu fitattun ‘yan siyasa da ke kurkuku afuwa kan laifin Rashawa.

Duk da cewa gwamnati a hukumance ba ta fitar da sunaye dukkanin mutanen da ta yi wa afuwa ba, akwai bayanan da ke nuna cewa cikin wadanda aka yi wa afuwa akwai tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame.

Tsofaffin gwamnonin sun kasance cikin mutum 159 da majalisar kolin ta yiwa afuwa wanda aka yankewa hukuncin dauri a gidan yari kan cin hanci da rashawa.

Tun da farko Naja’atu Muhammad ta shaidawa sashen Hausa na gidan rediyon Faransa cewa batun afuwar sam bai dace ba kuma ba ya bisa tafarkin doka.

Gwamnati ba ta kyauta ba, dan sabo dai ya kamata shi shugaban ƙasa ya gane dukiyar nan ba ta sa ba ce dukiyar al’umma ce”.

“Kuma ita gwamnatin tarayya ba hurumin ta ba ne yin yafiya (Amnesty) ga laifuffukan da su ka shafi jiha, jiha ce ya kamata”.

Ta ƙara da cewa “Buhari ya tabbatarwa da jama’a cewa shi ba mai riƙe amana ba ne kuma shi ba mai tabbatar da alkawari ba ne”.

“Duk alƙawarin da Buhari ya yiwa ƴan Najeriya musamman ƴan arewa da su ka zaɓe shi su ka bi shi su ka rasa rayukansu da dukiyoyin su. Duk amanar da su ka ba shi ya ci ta, babu ɗaya da ya cika”. In ji Naja’atu Muhammad

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button