Labarai

Buhari ya ba da umarnin raba tan 40,000 na hatsi ga mabuƙata domin bukukuwan Easter da Sallah

 

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da a gaggauta fitar da tan 40,000 na hatsi iri daban-daban da ga rumbun gwamnati domin taimakawa marasa galihu a Nijeriya wajen gudanar da bukukuwan Easter da Sallah masu zuwa.

Ministan Noma da Raya Karkara, Muhammed Mahmood ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati bayan ganawar sirri da Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Talata.

Daily Nigerian hausa ta ruwaito mahmood, ya ce shugaban kasar ne ya gayyace shi tare da umartar sa da ya raba kayayyakin ga mabuƙata, inda ya kuma bayyana fatansa na cewa hakan zai rage raɗaɗin hauhawar farashin hatsi a kasuwa.

A cewarsa, ton 12,000 daga cikin tan 40,000 da aka amince da su, za a baiwa ma’aikatar kula da jin kai da bala’o’i da ci gaban jama’a ta tarayya domin rabawa ‘yan gudun hijira a fadin kasar nan.

“Na zo nan da yammacin yau ne sakamakon sammacin da shugaban kasa ya yi masa.

“Ya ba da umarnin kuma ya amince da fitar da hatsi daga Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Tarayya,” in ji Mista Mahmood yana cewa.

“Don a sanya hatsi a araha ga mutane don yin bukukuwan – Ramadan, Ista da Sallah.

“Za mu kuma ba da wasu hatsi ga ma’aikatar jin kai, don yin rabon.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button