Budurwa ta turo miliyoyin kuɗi daga ƙasar waje a gina mata gida a Najeriya, ta dawo ta ga kango
Wata budurwa ‘yar Najeriya mazauniyar ƙasar waje, ta ƙadu matuka da abinda ta gani bayan ta dawo gida Najeriya.
Budurwar ta turo maƙudan kuɗade domin a gina mata gida
Legit.ng ta samo daga wani shafin Instagram @gossipmilltv cewa budurwar ta turo miliyoyin naira gida lokacin da ta ke a ƙasar wajen domin gina gidan kan ta.
Ta cigaba da turo kuɗaɗe bayan ta gamsu ta rahoton da wanda ta wakilta gina gidan ya ke bata a koda yaushe.
Daga baya ta gane cewa cutar ta aka yi
Sai dai budurwa ta dawo daga ƙasar waje inda ta fahimci cewa ashe yaudarar ta akayi.
Ta fahimci cewa abinda wanda ta wakilta gina gidan ya ke faɗa mata ba haka bane a yayin da ziyarci wajen inda ta koka akan halin da wajen yake ciki.
An jiyo ta a cikin wani faifan bidiyo a yayin da ta kai ziyara wajen, ta na ta tambayar ina aka ajiye kwanon rufin da aka ce mata akwai.labarun hausa na wallafa a shafinta.
Ga bidiyon nan ƙasa:
View this post on Instagram
Mutane sun tofa albarkacin bakin su kan lamarin
@damiilaaree ya ce:
Mutum ya siya gida a ƙasar waje kawai idan ya na da hali, idan ya koma ƙasar ta asali a lokacin hutu yayi aikin ginin gidan sa da kan shi kawai.
@official_no_worries_yrn ya ce:
Idan na turo ma mutum kuɗi ya gina min gida sannan na zo na taras ba gidan, ba damuwa matar ka ko mijin ki ba za su gan ka ba.
@iam_ochai ya ce:
Ba ki yi murna ba ma kin taras da kango. Kawu na ko fili bai gani ba bayan ya gama tunanin an kammala gina mi shi katafaren gida. Tun waccan shekarar har yanzu bai farka daga sumar da yayi ba.