[Bidiyo] Jana’izar Inter-faith Daga Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyan Lemo
~Tarihin Kafuwar Inter-faith, Ma’anar Kalmar, Manufofinta Ko Abin Da Takeson Cimma lalle Mal. Bai Ha’inci Ilimiba Allaah Ya Kara Masa Daukaka.
~Inter-faith Yaudarace Ga Musulmi, Sharrice Ga Musulmi, Bata Lokacin Banzace yaa Allaah Ka Mana Tsari Da Aqidar Inter-faith Ka Kwato Bayinka Wadan Da Suka Bata Sanadiyyar Inter-faith.
A cikin wannan Video kashi na daya, Dr Sani yayi kaca-kaca da akidar nan ta interfaith wanda Nura Khalid yake tallatata.
A kwanakin baya, anan Facebook Nura Khalid yayi rubutu akan sam bai dace a Kira, kiristoci da kafirai ko arna ba, saidai a kirasu da Ahlul-kitab, inji Nura inda akayi ta kai ruwa rana dashi ya tsaya ya cure ya kuma rushe ayoyin alkur’any da suka nuna haka.
Dr Sani yace, “Akwai wadanda suke nuna cewa,, baya halatta a kira kafirai musamman Ahlulkitab wai musulmi bazai kirasu da kafirai ba, Dr yace ” yanzu akidar haka tayi yawa, a Al-alamul islami, ana kokarin cusawa musulmai cewa, “Zafin Kai ne da tsattsauran ra’ayi ne ka dubi wani kace masa kafiri, “yace masu fadan haka harda rawani na malanta.
Dr Sani can cikin cikin video yaci gaba da cewa “Yayin da Allah yace, ” Wadanda sukace Allah uku sun kafirta” Dr yace, “yayin da kace Allah yace duk wanda yace Allah uku ya kafirta, sai wani yace aa basu kafirta ba, waye yakewa martani? Allah ne!.
Wallahi raina ta kara samun natsuwa akan jawabin marigayi Sheikh Albani Zaria lalle Nura Khalid cikakken dan interfaith ta wahdatul adyan.
Domin nima shaida ne, anan Facebook Nura yazo yana rushe ayoyin Allah akan lalle a daina kiran arna da kafirai saidai Ahlul-kitab, babu shakka Dr Sani ya kara haska mana wadan nan mugayen bayi da suke labewa da malanta suke tabka mana barna.
Muhammad Ismail Ali.
Ga bidiyon nan kasa.