Labarai

Bana ‘Yan Crypto Za Su Kudance, Bitcoin Zai Kai Milyan 41 Inji Masana

Advertisment

An yi hasashen cewa, kudi mafi daraja a kasuwar crypto wato bitcoin zai haura zuwa kusan Naira miliyan 41.2 (dalar Amurka 100,000) a cikin shekara guda, a cewar shugaban kamfanin Nexo, wani babban kamfani na crypto a duniya.

A wata hira da CNBC, Antoni Trenchev ya ce ya yi imani da cewa, bitcoin zai iya tashi sama da $100,000 a cikin watanni 12.

Bitcoin zai ninka a farashinsa nan ba da jimawa ba; a cewarsa, ya damu matuka game da makomar bitcoin a cikin gajeren lokaci yayin da babban bankin Amurka, wanda yake daidai da CBN na Najeriya, ya fara kaddamar da wani shirin da zai sa crypto ya fadi ya tafi daidai da kasuwanni na yau da kullum.

Amma ya kara da cewa shirin na kasar Amurka kuma zai iya ba da kuzari ga farashin bitcoin a duniya.

Advertisment

Wannan yana nufin cewa farashin bitcoin zai iya shillawa sama fiye da ninki biyu a wannan shekara, idan zaton tsinkayar Trenchev ta zama daidai.

Ya yi hasashe a watan Janairu cewa farashin bitcoin zai kai dala 50,000 a karshen shekarar 2022. Ya ce mutane sun sha yi masa masa ba’a kan hasashen nasa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button