Labarai

Azumi: Rundunar Ƴan Sanda ta hana yin tashe a Kano

Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kano ta hana yin wasan tashe a Jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa bisa al’ada, idan azumin watan Ramadan ya kai kwana 10, akwai al’adar tashe da kuma kidan gwauro da yara da matasa ke gudanarwa a ƙasar Hausa.

Sai dai kuma a wannan shekarar ma, rundunar ta ce babu buƙatar yin hakan, kuma tayi gargaɗi mai zafi ga duk wanda ya fito ya aiwatar da wasan.

Kakakin rundunar ta jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Kiyawa, wanda ya fitar da sanarwar a madadin Kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, yace an dakatar da wannan al’ada ne ta tashe sabo da gudun kada ɓata-gari su yi amfani da wannan dama domin aikata ayyuka marasa kyau.

Ya kuma ƙara da cewa hanawar ta zo ne domin kada ƴan daba, masu kwacen waya da kuma ƴan shaye-shaye su yi amfani da wannan dama su illar al’umma.

SP Kiyawa ya yi kira ga iyaye da su tabbatar ba su bar ƴaƴan su sun karya dokar ba, inda yai gargaɗi cewa duk wanda a ka kama ya karya doka, ba shakka doka za ta yi aiki a kan sa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button