An ɗaura auren jaruma Nafisa Ishak wacce ta zagi Sheikh Aminu Daurawa
Jarumar Kannywood Nafisa Ishak ta angwance ita da mijinta.
An wallafa bidiyon auren Nafisa Ishak
A wani faifan bidiyo da tashar Duniyar Kannywood ta wallafa na bikin jaruma Nafisa Ishak, an nuna mijin da ta aura suna nunawa junan su shaukin ƙauna.
Haka kuma a cikin bidiyon an nuna wani wuri inda anan ne aka ɗaura auran jarumar da mijin na ta.
Ita kanta jaruma Nafisa Ishak ta wallafa bidiyon ta angon na ta a shafin ta na Tiktok da Instagram tana faɗin “Alhamdulillah.

Ta goge duk wata wallafar da tayi a baya
Sannan kuma jarumar ta goge duk wata wallafa da tayi a baya inda ta bar kawai na ɗaurin auren da kuma wanda ake kai ta ɗakin miji.
A kwanakin baya dai Nafisa ta tsinci kanta cikin wata taƙaddama bayan tayi raddi ga shahararren malamin addinin nan Sheikh Aminu Daurawa.
Raddin da ta yi ga malamin ya sanya ta sha suka a wajen mutane da dama wanda hakan ya sanya dole ta yi wani bidiyo inda ta bayar da hakuri.
Muna yi mata fatan alkhairi da fatan Allah ya bada zaman lafiya.labarunhausa na ruwaito.