AddiniLabarai

Allahu Akbar: matashin Alaramma ya karba kiran Ubangiji yana bada Sallah tahajjud

Legit.ng Hausa ta samu labarin rasuwar wani Alaranma mai suna Sani Lawal wanda ya rasu a lokacin da yake ibadar sallar dare a watan Ramadan.

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga majiyoyi da dama, Sani Lawal ya rasu ne a daidai lokacin sujada, yana limancin sallar tahajjud a ranar Asabar dinnan.

Tuni dai aka yi jana’izar marigayin dazu da safe da kimanin karfe 8:00 na safe a unguwarsu da ke Layin MB, Samaru, karamar hukumar Sabon Gari, Kaduna.

Wani Aminin Marigayin yace ya bar masallacin bayan an yi raka’a takwas. sai kurum aka kira shi a waya, aka fada masa ai Liman ya fadi a yayin sujuda.

Legit.ng Hausa tuntubi wani abokin marigyain, wanda ya shaida mana wannan labari mara dadi.

Malam Anas Mansur ya san Marigayin, kuma ya tabbatar mana da cewa ya rasu ne bayan ya yi sujudar tilawar Al-kur’ani da ke cikin surar nan ta Al-Nahli.

Mutumin Allah ne
A cewar Anas Mansur, kamar yadda ya yi bayani a Facebook, Marigayin mutumin kirki ne wanda al’ummar unguwar Samaru suke matukar bukatar ire-irensa.

Sani Lawan ya samu shaidar cewa yana cikin matasan da ke yi wa yara masu tasowa tarbiya.

“Allah ya azurta shi da kyakkyawan karshen kamar yadda Allah SWT Ya ce duk wanda suke sallah a wani bangaren dare za su tashi a cikin masu kololuwar daraja a Aljannah.”
Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur’ani a Sweden
Amin.

Ana yi Liman kyakkyawan zato

Aliyu Abubakar Zazzau wani abokin Marigayin ne, wanda ya tabbatar da rasuwarsa a shafinsa. Zazzau ya ce Alaranman ya rasu ne ya limancin sallar dare.

Amal Abubakar yake cewa ya samu labarin rasuwan malamin a cikin wannan wata mai alfarma. Amal ya ce irin wannan karshe na Sani Lawal abin madalla ne.

A halin yanzu jama’a su na ta aika sakon ta’aziyyarsu ga ‘yanuwansa da dalibansa da daukacin mutanen Unguwar Samaru, tare da rokon samun irin cikawarsa.

Watan Ramadan shi ne watan da ya fi kowane daraja da falala a addinin musulunci. Sannan kuma dare musamman irin na jiya yana daga cikin mafi daraja.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button