Alhazai miliyan 1 ne za su yi aikin Hajjin bana — Saudiya
Hukumomi a Saudi Arebiya sun sanar da cewa alhazai miliyan daya ne za su gudanar da ibadar aikin hajjin bana.
Hukumar Hajji da Umara ta ƙasar ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar, wacce shafin Haramain Sharifain ya wallafa, inda hukumomin su ka bayyana sharuɗɗa da za a bi domin gudanar da ibadar.
Sanarwar ta ce hukumar ta amince mutane miliyan daya daga ciki da wajen kasar su gudanar da aikin Hajjin na bana, amma, s cewarta, bisa sharadin bin matakan kare kai daga annobar korona, wacce ita ta hana gudanar da ibadar a 2020 da 2021.
Daga cikin sharuɗɗan, ma’aikatar ta ce ba za ta bari dattawan da suka haura shekaru 65 a duniya su gudanar da ibadar ba a bana.
Daily Nigerian hausa ta ruwaito Sannan, duk wanda zai shiga ƙasar sai an yi masa gwajin korona na aƙalla awanni 72, wato kwanaki 3, kafin ya shiga kasar ta Saudiyya.
Sanarwar ta kara da cewa dole ne duk maniyyaci sai ya yi cikakken adadi na allurar rigakafin korona, wadda kasar Saudiyya ta amince da ita, da kuma bin sauran matakan kula da lafiya kamar yadda a ka saba.