Aisha Buhari ta gayyaci ƴan takarar shugaban ƙasa shan ruwa a villa amma kada kowa ya je da waya
Uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari ta gayyaci ƴan takara shugabancin ƙasar nan daga jam’iyyu daban-daban zuwa shan ruwa a Fadar Aso Rock Villa a ranar Asabar.
Aisha Buhari ta miƙa gayyatar ne ga dukkan ƴan takara daga dukkan jam’iyyun kasar.
Cikin wani rahoto da ta wallafa, tashar talabijin ta Channels ta ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da sauran ƴan takarar shugabancin ƙasa ne za su halarci taron kawai
Akwai kuma ‘yan takara 17 daga babbar jam’iyyar PDP mai adawa – kamar gwaman Nyesom Wike na jihar Rivers, da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da sauran ‘yan takara daga jam’iyya mai mulki ta APC, NNPP, ADC, APGA da sauran su.
Wani abu da ya ja hankulan mutane shi ne katin gayyatar zuwa shan ruwan, domin a ciki an bukaci dukkan wadanda aka gayatar su guji zuwa da wayoyinsu na hannu zuwa shan ruwan, kuma katin ne zai ba su damar shiga Fadar Shugaban Najeriya.