Labarai

2023: Ni zan fara yin Mataimakiyar Shugaban Ƙasa — Yahaya Bello

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce zai ɗauki mace ta yi masa mataimakiya idan jam’iyar APC ta tsaida shi takarar shugaban ƙasa a 2023.

Bello ya baiyana hakan ne a wani taron karawa juna sani da ƴan jarida masu rahoton labaran siyasa da na kotu a jiya Juma’a a Abuja.

Daily Nigeria hausa na wallafa a cewar Bello, zai baiwa mata muhimmanci idan har a ka bashi dama ya zaɓi wanda zai yi takara da shi.

Gwamnan ya ce ya na da burin yin gwamnati da za ta tafi da kowa, musamman mata, matasa da masu buƙata ta musamman.

Ya ƙara da cewa haka ya ke gudanar da mulkinsa a Kogi in da bai bar kowa ba wajen tafiyar da gwamnatinsa.

Bello ya ƙara da cewa idan ya samu dama, zai samar da tallafi ga matasa da mata domin bunƙasa tattalin arziki.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button