Labarai

Ƴan sanda sun kama wani mutum da ɗauri 250 na wiwi a Kano

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano a jiya Asabar ta kama wani matashi mai shekaru 33 da haihuwa, mai suna Agbo Victor da ke fataucin miyagun kwayoyi, ɗauke da ɗauri 250 na tabar wiwi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a Kano.

Daily Nigerian hausa ta ruwaito ya ce jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake tafiya a cikin wata mota makare da yanar wiwin a Kwanar Dangora a Ƙaramar Hukumar Kiru ta jihar.

HlKiyawa, ya ce wanda ake zargin ya dauko kayan ne daga Edo zuwa wani dillalin miyagun kwayoyi da ke Kano, wanda yanzu haka ya tsere.

Ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, Samaila Shuaibu Dikko, ya bayar da umarnin mika shi zuwa sashin binciken miyagun kwayoyi na sashin binciken manyan manyan laifuka na rundunar domin bincike mai zurfi.

Kakakin ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA