Zamfara: PDP ta farga da hukuncin Ebonyi, inda ta garzaya kotu domin a sauke Gwamna Matawalle
Babbar Kotun Taraiya da ke Abuja ta sanya ranar 7 ga watan Afrilu domin sauraron ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar gabanta, inda ta ke son a sauke Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle da ga mukaminsa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, PDP a Zamfara ta shigar da ƙarar ne kwanaki biyu bayan da kotun ta sauke Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi da ga muƙamin sa.
Sai dai Umahin ya ƙi sauka, inda ya ɗaukaka ƙara, ya kuma bugi ƙirji cewa babu wata kotu da ta isa ta sauke shi da ga Gwamna.
A yau Alhamis, Alkalin Babbar Kotun Taraiyar, Mai Shari’a Inyang Ekwo, wanda shi ne ya bada umarnin sauke Umahi, ya karbi takardar karar.
Cikin takardar ƙarar da PDP ta mikawa kotun, ta nemi da a rantsar da tsigaggen Mataimakin Gwamnan gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau a matsayin gwamna.
Hakazalika PDP ta buƙaci a sauke ‘yan majalisar tarayya da na jiha su kimanin 37 sabo da sun sauya sheƙa zuwa APC.