Labarai

Za a yi aikin Hajjin bana tare da ƴan ƙasashen waje – Saudiya

Za a yi aikin Hajjin bana tare da ƴan ƙasashen waje - SaudiyaƘasar Saudi Arebiya ta tabbatar da cewa za a yi aikin Hajjin bana tare da alhazzai da ga ƙasashe a faɗin duniya.
Shafin yanar gizo na Haramain Sharifain ne ya wallafa sanarwar a yau Lahadi, inda ya baiyana cewa Ma’aikatar Hajji da Ummara za ta ware adadin alhazan ko wacce ƙasa.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa bayan an shafe shekaru 2 ba a yi aikin Hajjin da ƴan ƙasashen waje ba sakamakon annobar korona, a bana, Masarautar Saudiyya ta baiyana cewa alhazai da ga ƙasashen waje za su yi aikin Hajji.
Sai dai Ma’aikatar ta shimfida sharadi cewa kowanne maniyyaci sai ya yi allurar rigakafin korona sannan zai samu damar zuwa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button