Labarai

Yanzu yanzu: Kotu ta soke belin Muaz Magaji Dan Sarauniya tare da bada umarnin a cafko mata shi

Yanzu yanzu: Kotu ta soke belin Muaz Magaji Dan Sarauniya tare da bada umarnin a cafko mata shiKotun majistare mai lamba 58 a jihar kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Aminu Gabari ta soke belin da tun farko ta baiwa mai sukar nan ta kafafen sadarwar zamani ga gwamna Ganduje wato Mua’zu Magaji wanda aka fi sani da Dansarauniya bisa rashin halartar kotun har sau 3 domin amsa tuhumar da ake masa na bata sunan gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Hakazalika kotun ta bayar da umarnin kama shi tare da sammaci ga wadanda suka tsaya masa mutum biyu da su bayyana a ranar 28 ga Maris, 2022 a kotu.
Jarida Radio
14/3/22

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button