Yadda Jaruma Maryam Yahaya ta dauki wanka mai zafi a wurin dinar tsohon saurayinta, Abubakar Mai Shadda
Yayin da ake shagalin bikin fitaccen furodusan Kannywood, Abubakar Bashir Mai Shadda, jaruma Maryam Yahaya, wacce tsohuwar budurwarsa ce ta ba kowa mamaki, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.
Hausawa su kan ce “kishi kumallon mata”, sai dai a bangaren Maryama Yahaya, ta nuna cewa sam ba hakan bane.
Domin ta bayyana a wurin bikin wanda aka kwashe ranaku da dama ana shagulgula iri-iri, inda ta dauki wanka mai burgewa.
Duk shagalin da aka yi sai da ta yi anko kuma ta nuna murnar ta ta hanyar girgijewa inda ta dinga tikar rawa wanda ya ba kowa mamaki.
Jarumai, mawaka da sauran mutane ‘yan uwa da abokan arziki sun yi cincirindo wurin zuwa bikin wanda aka dinga barin nairori.
Manya a industiri irin su Ali Nuhu, Rarara, Adam A. Zango da sauran su duk sun yi masa kara wanda hakan yasa bikin ya dauki hankali kwarai.
A bangaren manyan mata kamar Saratu Gidado wato Daso, Teema Makamashi, Hadizan Saima da sauran su duk sun halarci bikin. Hatta tsofaffin jarumai kamar su Fati Bararoji, Masura Isah duk sun je.
Sai dai lamarin bai bayar da mamaki ba saboda wannan ne karo na farko tsawon lokaci da dan fim ya auri ‘yar fim, hakan yasa kowa yake mararin zuwa don shagali ne na tuwo na mai na ne,labarunhausa na tattaro bayyanai.
Bayyanar Maryam Yahaya, tsohuwar budurwar ango ya yi matukar ba mutane mamaki, saboda ba a yi tunanin zata je ba saboda wasu dalilai.
Tun da aka fara shirye-shiryen bikin mutane suka dinga tsegunguma har ta WhatsApp akan cewa ba a ga Maryam Yahaya ta wallafa katin gayyata ko kuma ta taya ma’auratan murna ba.
Wasu suka dinga tambayar cewa ko dai kishi ne ya hana ta wallafawa saboda kusan duk wasu ‘yan masana’antar suna ta wallafawa tare da yi musu fatan alheri.
Kwatsam sai ga Maryam Yahaya sanye da ankon bikin cike da murna inda ta bayyana a wurin shagalin wanda hakan ya yi matukar bayar da mamaki.
Ta wallafa hotunan a shafinta na Instagram:
View this post on Instagram
Sai dai a bangaren rawa ba ta zake ba balle ace ta yi wani abu saboda kishi ko kuma bakin ciki.
View this post on Instagram
Kuma ta wallafa hotunan angon tayi masa fatan alkhairi
“Allah yasanya alkhairi Allah yabaku zaman lfy @realabmaishadda”
View this post on Instagram