Yadda Aka Kama Fasto Ya Yi Wa Karamar Yarinya Fyade
Kotu ta tsare wani limamin coci mai shekara 55 da aka kama kan yi wa wata karamar yarinya fyade.
Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Insfekta Oriyomi Akinwale, ya shaida wa kotun cewa Fasto Rufus Oyediran ya yi wa karamar karamar yarinyar fyade ne bayan ya tare ta a gidansa.kamar yadda aminiya trust na ruwaito
Ya ce a lokacin da yariyar mai shekara 13 take wucewa ta gidan ne faston ya kira ta, daga baya ya tube ta tsirara ya sadu da ita.
Insfekta Oriyomi Akinwale, ya ce ’yar uwar yarinyar, wacce tagwai dinta ce ta kai kara ga kakarsu da suke zaune da ita, bayan ta ga fitowarta daga gidan faston.
Bayan nan ne Alkalin kotun, Bankole Oluwasanmi, ya ba da umarnin tsare Fasto Rufus a gidan yari da ke Ado-Ekiti, bayan an gurfanar da shi a gabanta kan zargin lalata karamar yarinyar a yankin Efon-Alaye na jiyar.
Alkalin kotun ya kuma bayar da umarnin tsare malamin addinin har zuwa ranar ranar 9 ga watan Afrilu, 2022 da kotun za ta ci gaba da sauraron shari’ar.