Yadda ƴan bindiga sunka ƙona magidanci da matarsa da ‘ya’yansu
A jiya ranar Alhamis yan bindiga sunkai hari a garin maikujera da ke karamar hukumar mulkin Rabah da ke jihar Sokoto.
Hausaloaded ta samu zantawa da wani mutum mazauni garin yana cewa abinda ya faru na kashe wannan bawan Allah da matarsa mai dauke da juna biyu da karamin ɗansu.
Magajinsa mutum ne da yake namomi a ciki garin maikujera wanda yake noma albasa kuma alhamdulillahi tayi kyau sosai to shine ya aika a saya kuma an sayar to shine jiya din wanda yake baiwa ya kawomasa kudi.
To shine dare nayi barayi sunka shiga cikin gidansu inda sunka tarar da gidan babu kudi, babu mai kudin, ya tsere duba da yasan tabbas tunda anka san an kawo masa maƙudan kudi za’a zo nemansa saboda akwai barazanar rashin tsaro.
To shine sunka bincike sunka tabbatar tabbas wanda sunka zo nema baya gidan, shine ƙanensa da matarsa mai juna biyu da ɗansa suna kwance cikin daki sunka bude sunka dauko harawa sunka kunna mata wuta sunka jefa a cikin dakin.
Wanda shine sanadiyar ƙonewarsu ƙurmumus subhanallah,Allah ya jikansu yayi musu rahama Amen.