Labarai

Wasu ‘yan mata a jihar Sokoto sun fito takarar Gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023

Wasu 'yan mata a jihar Sokoto sun fito takarar Gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2023Matashiya Farida Labaran Yusuf ta bayyana ra’ayin ta na tsayawa takarar Gwamnan jihar Sokoto a zaben 2023 da ke tafe a karkashin jam’iyar PDP mai ci a jahar Sokoto.
Farida labaran Yusuf har ta mayar da shafinta na sada zumunta wato Facebook excellency Farida labaran yusuf harka bada wasa ba.
A bangare daya, Farida Labaran ta zabi yar uwar matashiya Hajaru Muhammad mai dambun kaza a matsayin mataimakiyar ta.
Su dai wadannan ‘yan mata sun fito takarar ne a jam’iyyar PDP mai alamar lema da ke jahar Sokoto.
Shin kuna ganin anya wadannan matasan ‘yan mata za su kai labari kuwa?
Shafin Nasara shine ya labarto wannan labari.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA