Labarai

Wani yaro Dan shekara 18 ya kashe wata mata da tabarya a kano

An kama yaron dan kimanin shekara 18 cif da haihuwa, da ake zargi da kisan wata mata dake Danbare ta karamar hukumar kumbotso ta jahar kano.
A yau ne Allah ya a jami’an tsaron yan sanda na jahar kano sa’ar kama Wanda ake zargi da kisan Rukayya mustapha, dake Danbare ta karamar hukumar kumbotso ta jahar kano.Wani yaro Dan shekara 18 ya halaka wata mata da tabarya a kano
Yaron dai Wanda shekarunsa kwatakwata basu haura shekara sha takwas ba a duniya, mai suna Abdussamadu suleiman Wanda ke a dorayi charanchi quarters.”
Yanzu haka dai sashin binciken manyan laifuka na yan sandan jahar kano dake banfai, suna Ci gaba da bincikar Wanda ake zargin.”
Abdulsamad suleman yana cewa

Na shiga gidan anty rukayya naje an kawo mata salaf sai taje ta kwanta da naga alamun sun fara barci sai naga wayoyi gudu ukku sai nayi tunani sai naje na dauko tabaryi sai na bubugawa anty rukayya sau biyu ‘ya’yanta kuma sau daya daya.

Sai na dauki wayoyin sai nayi sauri na futa ina fita sai ga muazzam sai yace minene sai nace babu komai wayoyi ne kawai na dauko sai muka tafi na bashi guda daya sai muka tafi gida sai dare yana yi naje na sayar da wayoyin”.

Na sayar da wayoyin daya dubu goma sha biyar dayan dubu biyar, nayi kudin mota zuwa garinmu sai na saya agogi guda biyu sai na bada naira dubu biyar a sayamin kaji,sai dubu biyar zan saya rake.

Anty rukayya kanwar baban mu ce da na buga mata tabarya akai nishi kawai ta dinga yi.

Ga hirar da Sunkayi nan da jiman tsaro.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button