Labarai

Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴan ta’adda 200 a Naija

Rundunar Sojin Nijeriya ta hallaka a ƙalla ƴan ta’adda 200 a wani sumame da sojojin su ka kai kan maɓoyar ƴan ta’addan a ƙauyen Ghana da ke Ƙaramar Hukumar Mariga a Jihar Naija.
Majiyar Daily Nigerian tace PRNigeria ta rawaito cewa ƴan ta’addan sun gamu da ajalin su ne a jiya Laraba bayan da jiragen yaƙin sojoji, karkashin rundunar sojin ‘Operation Thunder Strike’ da ‘Operation Gama Aiki’ su ka yi musu luguden wuta ta sama.
Rahoton ya ce an kai wa ƴan ta’addan sumamen ne da misalin ƙarfe4:45 da kuma karfe 6:34 a wasu sansanonin su da ke Ghana.
PRNigeria ta rawaito cewa an daɗe a na fakon ƴan ta’addan, inda a ka gano cewa sun kasa kan su zuwa rukuni-rukuni na a ƙalla mutum 40 kuma da baburan ashirin da biyar-biyar.
A maimakon dakarun su yaƙi rukuni-rukuni daban-daban na ƴan ta’addan wanda hakan ba lallai a samu abinda a ke so ba, sai su ka haƙura su ka ci gaba da fakon su har sai da su ka haɗu a waje guda a yankin Ghana, inda sojojin su ka afka musu, su ka hallaka 200 a cikin su.
Wata majiyar sirri da ga ɓangaren sojoji ta ce a ƙalla ƴan ta’adda 150 sun hallaka nan take a harin.
Majiyar ta ƙara cewa waɗanda su ka tsere da raunuka a jikin su, sai sojojin ƙasa kuma su ka afka musu su ka gama da su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button