Labarai

Shugaban jam’iyar NNPP na maraba da Kwankwaso, amma ya ce babu tabbacin takara ga sabbin zuwa

Advertisment

Shugaban jam’iyyar NNPP, reshen Jihar Kano, Hisham Habib ya ce jam’iyyar na maraba da kowa amma ba za ta ba da tabbacin tikitin tsayawa takara ba.
Shugaban jam’iyyar ya kuma bayyana aniyarsa ta karbar sabbin masu shigowa jam’iyyar a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.Shugaban jam'iyar NNPP na maraba da Kwankwaso, amma ya ce babu tabbacin takara ga sabbin zuwa
Daily Nigerian ta ruwaito a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, Habib ya ce jam’iyyar za ta yi aiki da kowa da ya shigo jam’iyar wajen cimma manufofin ta.
“Muna bayyana fatanmu da hangen nesa na inganta Kano da Najeriya inda za a bai wa ‘yan kasa dama daidai gwargwado.
Shugaban ya kuma bayyana cewa ‘ya’yan jam’iyya na asali ka iya tsayawa takara kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.
Shugaban jam’iyyar na jiha ya kuma yi godiya ga shugabannin jam’iyyar tun daga matakin shiyya har zuwa matakin kasa bisa kokarinsu na ciyar da ita gaba.
Habib ya bayyana haka ne yayin da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso ke shirin sake ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.
Sakataren NNPP na kasa mai barin gado, Ambasada Agbo Gilbert Major ne ya bayyana hakan a Abuja, a yammacin ranar Talata.
‘Tuni Sanata Kwankwaso a ranar Talata ya gana da shugabannin jam’iyyar NNPP a yunkurinsa na ganin ya kammala zuwansa jam’iyyar da ake sa ran zai yi amfani da shi wajen neman takarar shugaban kasa.
Sai dai kuma yayin da yake mayar da martani game da labarin cewa Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar daga PDP, Habib ya ce shugabannin jihar Kano suna sa ran hedkwatar kasa karkashin jagorancin Dakta Boniface Aniebonam ta tsara duk wani hadaka da ko kawance da kungiyoyin da ke shigowa jam’iyyar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button