Labarai

Shin da Gaske Gwamnatin Zamfara ta baiwa Bello Turji Mota kirar Hillux ta kimanin miliyan ₦30M ?

Advertisment

Rahotani sun ta yawo a kafafen sada zumunta cewa bello turji ya tuba har gwamnatin jihar Zamfara ta bashi kyauta danƙareriyyar mota ta naira miliyan ₦30m kamar yadda wani shafi mai suna Zamfara online Gusau na wallafa.

Rahotanni daga Zamfara Sun tabbatar Gwamantin Jahar ta yiwa Shugaban ‘yan Tadda Bello Turji kyautar Dalleliyar mota kirar hellux ta kimanin Miliyan 30.

Wasu mazauna Kauyukan Fakai da kware dake Cikin Karamar Hukumar Shinkafi Sun tabbatar da gaskiyar Rade radin kyautar mota ga Shugaban Mahara mafi Shahara a Arewacin Najeriya. Kamar yadda Wani Mazaunin Kauyen Jangeru ya shedawa Jaridar Zamfara online Cewa Ranar Laraba Shugaban Rundunar ‘yan Ta’addan Daji Bello Turji ya Kai Ziyarar a garin na Jangeru Cikin Sabuwar motar tare da Rakiyar Baburan yaransa kimanin Ashirin gabansa da bayansa Cikin Shirin Kota kwana.

Mazauna Kauyukan Sunce Motar kirar Hellux Sabuwa dal wacce darazar kudinta Zai iya haura Miliyan 30, suna Zargin Gwamanan Jahar Zamfara ta Hon. Bello Muhammad Matawalle ce tayi kyautar Motar ga Kachalla Turji.

Advertisment

Wasu na ganin kyautar Motar nada alaka da takaituwar hare haren Maharan a kauyuka da Hanyoyin a jahar ta Zamfara..

Majiyarmu ta samu wani labarin da ke editan jaridar daily trust Abdulaziz Abdulaziz wanda yayi hira da bello turji ya fadi gaskiyar maganar ga abinda yake cewa.

“Aikin jarida aiki ne da yake buƙatar tabbatar da gaskiyar abinda mutum ya ji, kafin wallafawa. Bana tsammanin wannan labari gaskiya ne (duk kuwa da cewa na san Turji na maganar sulhu da jami’an gwamnati).
Gaskiyar maganar ita ce: Turji ya mallaki motocin Alhaji Auta (wanda aka kashe kwanakin baya), Hilux guda biyu da wasu kayayyakinsa, kamar yadda wani makusancin Alhaji Auta ya labarta min a makon jiya.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button