Labarai

RAHOTO: Harin jiragen yaƙi ya hallaka Shugaban ISWAP, Sani Shuwaram kuma har sun naɗa sabo

Advertisment

Wani harin jiragen sama da Rundunar sojin Nijeriya ta kai ya yi sanadiyyar mutuwar fitinannen Shugaban Ƙungiyar ISWAP, Sani Shuwaram da sauran mayaƙansa a yankin Marte, in ji rahoton jaridar PRNigeria.
Rahoton ya ce jiragen yaƙin nan masu suna Super Tucano da sauran jiragen Rundunar Sojin Sama, NAF ne su ka yi wa sansanin Shuwaram ɗin luguden wuta.

RAHOTO: Harin jiragen yaƙi ya hallaka Shugaban ISWAP, Sani Shuwaram kuma har sun naɗa sabo
RAHOTO: Harin jiragen yaƙi ya hallaka Shugaban ISWAP, Sani Shuwaram kuma har sun naɗa sabo

Rahoton ya ƙara da cewa Shuwaram ya rasu ne bisa harin bindiga da jiragen yaƙin su ka riƙa zubo wa, inda ya samu muggan raunuka har su kai sanadiyyar mutuwarsa a Sabon Tumbuns da ke Tafkin Chadi.
Hakazalika wasu majiyoyi na tsaro sun tabbatar da harin da yayi sanadiyar kisan Shuwaram ɗin.
PRNigeria ta biyo cewa tuni kungiyar ta ISWAP ta naɗa sabon shugaba mai suna Bako George domin ya gaji Shuwaram.
Sources : Daily Nigerian Hausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button